Synopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodes
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
08/11/2024 Duration: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ko meke haifar da tarnaƙi a tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya?
22/10/2024 Duration: 04minRa'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali kan yadda aka kwashe watanni biyu bayan da shugaban kasa ya umarci hafsoshin tsaro da su tare a jihar Sokoto don tabbatar da tsaro, amma har yanzu 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa. Shin ko me ke haifar da tarnaki ga kokarin tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
18/10/2024 Duration: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ra'ayoyi: Najeriya za ta shafe shekara 100 kafin magance talauci
17/10/2024 Duration: 10minBankin Duniya, ya ce Najeriya da wasu ƙasashe da dama masu tasowa, za su iya shafe tsawon shekara ɗari a nan gaba kafin su yi nasarar rage kaifin talauci da ke addabar al’ummominsu. Wannan gargaɗi na Bankin Duniya na zuwa ne a daidai lokacin da bayanai ke cewa kusan a kowace rana ta Allah ana samun karuwar mutanen da suka dogara da malauna ne domin samun abin da za su ci da kuma iyalansu.Shin, ko yaya za ku bayyana matsayin talauci ko fara a inda ku ke rayuwa?Ko kun gamsu da irin matakan da hukumomin ƙasashen ke ɗauka domin rage kaifin talauci a tsakanin al’umma?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kaurace wa karawa da Libya da tawagar Najeriya ta yi
15/10/2024 Duration: 10minShirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan rana ya maida hankali ne kan yadda tawagar kwallon Najeriya Super Eagles ta kaurace wa buga wasa da takwararta ta Libya sakamakon taskun da suka ci karo da shi lokacin isarsu a lasar ta Libya. Tuni gwamnatin Najeriya ta gayyaci jakadan Libya da ke Abuja don bayyana rashin amincewa da yadda aka tozartar da ƴan wasan na Super Eagles, lamarin da ake ganin cewa ya fara daukar sabon salo daga wasanni zuwa siyasa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin........
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kwace wa mutane 9 shaidar zama ɗan ƙasa a Nijar
14/10/2024 Duration: 09minGwamnantin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace wa mutane 9 dukanninsu makusanta ga hamɓararren shugaban kasar Mohamed Bazoum shaidar zama ɗan ƙasa saboda zarginsu da shirya wa ƙasa zagon-ƙasa. Tsohon madugun ƴan tawaye Rissa Ag Boula da kuma Janar-Janar biyu na soji na daga cikin waɗanda wannan mataki ya shafa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
11/10/2024 Duration: 10minA kowacce ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar tofa albarkacin bakinsu dangane da batutuwan da ke ciki musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur da kashi 15 cikin 100
11/10/2024 Duration: 10minNajeriya ta yi sabon ƙarin farashin mai da akalla kashi 15%, wanda kuma shi ne karo na 4 a cikin watanni 16 da shugaba Bola Tinubu ya shafe kan karagar mulki. Babu dai wani dalili da kamfanin NNPCL da ke matsayin wakilin gwamnati a harkar mai ya bayar dangane da wannan farashi, illa kawai jama’a sun gan shi ne haka kwatsam.Kan wannan batu shirin 'Ra'ayoyin Masu Sauraro' na ranar Alhamis ɗin nan ya bayar da damar tattaunawa akai.
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan ribar da bankunan Najeriya ke samu duk da ƙuncin rayuwa
09/10/2024 Duration: 10minA Najeriya, yayin a ke fama da matsalar tattalin arziki da tsanantar harkokin rayuwa, alkaluma na tabbatar da cewa bankunan ƙasar na ci gaba samun gagarumar riba a kowace rana ta Allah. Shin ko meye dalilin wannan gibi tsakanin bankuna da kuma al’umma? Wane gyara ya kamata ayi domin tabbatar da cewa arzikin kasa na zagayawa a cikin al’umma? Wannan shine maudu'in da masu sauraro suka tattauna akai.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ingancin dimokuraɗiyya a Najeriya
08/10/2024 Duration: 09minA Najeriya, yanzu haka wasu sun fara nuna fargaba a game da yadda tsarin dimokuradiyya ke gudana a kasar, musamman lura da yadda da zarar aka gudanar da zaben kananan hukumomi, to ko shakka babu jam’iyyar da ke rike da kujerar gwamna ce za ta lashe zaben babu tantama. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka bai wa kananan hukumomin damar cin gashin kansu.Abin tambaya anan shi ne, me ya sa a kullum jam’iyya mai rike da mukamin gwamna ce ke lashe zaben kananan hukomomi a Najeriya?Meye tasirin hakan game da fatan da ake da shi na ganin cewa al’umma ta morewa tsarin dimokuradiyya daga tushe?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ra'ayoyin masu saurare kan rikicin Gaza da ke cika shekara guda
07/10/2024 Duration: 09minYau 7 ga watan oktoban shekarar daya kenan da mayakan Hamas suka kaddamar da hare-hare a Isra’ila, inda suka kashe mutane 1 da 200 tare da yin garkuwa da wasu akalla 150. Wannan ya fusata Isra’ila inda ta mayar da martani ta hanyar kashe sama da mutane kusan dubu 43 a yankin Gaza, tare da yaduwar wannan rikici zuwa kasashen Lebanan da Iran.Shin me za ku ce a game da wannan lamari da ke kara jefa cikin zaman zullumi?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
Ra'ayoyin masu saurare kan tsadar farashin litar fetur
17/09/2024 Duration: 09minAna iya cewa murna na neman komawa ciki a Najeriya, bayan da aka yi hasashen cewa da zarar Dangote ya fara shigar da tataccen mai a kasuwa zai wadata sannan akan farashi mai rahusa. To sai dai ranar farko da fara shiga da man na Dangote, sai kamfanin NNPCL ya sanar da ƙara farashin mai a kasar.Shin ko me za ku ce a game da wannan sabon karin faraashin mai wanda shi ne karo na uku cikin shekara daya a Najeriya?Ko meye dalili karuwar farashin mai a Najeriya duka da cewa ana hakowa da kuma tace shi ne a cikin gida?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan bikin maulidi
16/09/2024 Duration: 10minYanzu haka al’ummar musulmi a sassan duniya na ci gaba da gudanar da bukukuwan Mauludi, domin tunawa da ranar da aka haifi annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah. Shin ko yaya matsayin wannan rana yake a gare ku?Ta wace fuska ku ke gudanar da bikin tunawa da wannan ranar?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyi: Belin miliyan 10 kan masu zanga-zangar yunwa a Najeriya
12/09/2024 Duration: 10minKotu a Abujan Najeriya, ta bukaci 10 daga cikin ɗimbin mutanen da aka kama suna zanga-zanga domin yunwa, da ya biya Naira milyan 10 a matsayin kuɗin beli kafin sallamar sa daga gidan yari. Shin ko ta ina wanda ke fama da yunwa zai fito da Naira milyan 10 domin ya beli kansa?To me zai faru idan har wani ko wasu suka taimaka da waɗanda kuɗade ba beli?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ambaliyar ruwa a Afrika
11/09/2024 Duration: 10minYamai babban birnin Jamhuriyar, ya fara karɓar baƙuncin taron ƙwararru da saurann masu ruwa da tsaki kan matsalar sauyin yanayi da ta shafe yankin yammacin Afrika. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sassan yankin na Yammacin Afirka da Sahel ke fuskantar Iftila’in Ambaliyar mafi muni da aka taɓa gani cikin aƙalla shekaru 20, kamar yadda aka gani a garin Maiduguri, inda a baya bayan nan saukar ruwan sama ya janyo tumbatsar dam ɗin da ya fashe, lamarin ya haddasa mummunar ambaliyar da ta mamaye sassan birnin da dama.Wane hali ake ciki a garin na Maiduguri bayan iftila’in da ya auku?Wadanne dabaru ya dace a bi wajen daƙile sake aukuwar haka, ko kuma rage girman barazanar da aka gani, ta hanyar karkatar da tarin ruwan da ke ambaliya zuwa ga amfanin jama’a?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
Ra'ayoyin masu saurare kan buƙatar Katsinawa su tashi su kare kansu
10/09/2024 Duration: 09minGwamnan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Malam Dikko Umaru Radda ya yi kira ga al’umma da ta jajirce wajen kare kanta daga hare-haren ƴan bindiga masu garkuwa da mutane, tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai don kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan komawa makarantun boko
09/09/2024 Duration: 09minA Najeriya, yau ake sake buɗe makarantun firamire da sakandare don fara karatu bayan dogon hutu da aka gudanar. Ana komawa makarantar ne a wannan karo a cikin wani yanayi na matsanciyar tsadar rayuwa wanda ya samo asali daga sabon ƙarin farashin mai fetur da aka yi a kasar.Shin a wane yanayi yaranku ke komawa makarantar a wannan litinin?Ko akwai wani sauyi musamman ta fannin farashin kayan karatu da kuma kudin sufuri?
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan batutuwa daban daban
06/09/2024 Duration: 10minRFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinku kan batutuwa daban daban da ke ci musu tuwo a ƙwarya a kowacce ranar Juma'a. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan tasirin taron China da Afrika
05/09/2024 Duration: 09minAn fara taron shekara-shekara don kyautata hulɗa tsakanin China da Afirka wanda ya samo asali kimanin shekaru 24 da suka gabata. Alƙaluma sun tabbatar da cewa China ita ce ƙasar da nahiyar Afirka ta gudanar da hulɗar tattalin arziki da kasuwanci fiye da kowace nahiya, yayin da a ɗaya bangare bashin da China ke bin Afirka ke ci gaba da ninkawa ninkin-ba-ninkin.Meye ra’ayoyinku a game da kamun lodayin China a fagen tattalin arziki, siyasa da kuma zamantakewa a nahiyar Afirka?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Alheri Haruna.
-
Yadda batun ci gaba da biyan tallafin mai a Najeriya ya janyo cecekuce
20/08/2024 Duration: 10minShirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan mako ya duba yadda ake fama da matsalar karancin main fetur a Najeriya, wasu bayanai na nuni da cewa yanzu haka gwamnatin ƙasar ta ware naira triliyan 6 da bilyan 800 a matsayin kuɗin tallafi mai a ƙasar.Bayanai sun ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne don biyan tallafin tun daga watan agustan bara har zuwa disambar wannan shekara ta 2024 wato wata watanni 17 cur. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara