Synopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodes
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
04/07/2025 Duration: 10minA duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Yadda wasu fitattun ƴansiyasa a Najeriya suka kafa wani sabon ƙawance
03/07/2025 Duration: 10minWasu fitattun ƴansiyasa a Najeriya, sun sanar da kafa wani sabon ƙawance da zummar ƙwace mulki daga hannu shugaba Bola Tinubu a shekara ta 2027. To sai dai abin lura a nan shi ne, waɗanda suka ƙulla ƙawancen mutane ne da suka taɓa riƙe muhimman muƙamai ƙarƙashin gwamnatoci daban-daban ciki har da ta APC. Abin tambayar shine, ko waɗanne irin alƙawura ne da za su sake gabatar wa 'yan ƙasar domin samun ƙuri’aunsu? Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kashe 'yan ta'adda da jami'ai su ka yi a Najeriya
02/07/2025 Duration: 10minA Najeriya, ga alama sabon salon da hukumomin tsaro na tarayya da kuma na jihar Zamfara su ɓullo da su, sun fara yin tarisi a yaki da ayyukan ƴanbindiga da suka addabi jama’ar yankin. Bayanai sun ce farmakin da ƴan sa-kai suka kai ƙarshen makon jiya, ya yi sanadiyyar mutuwar ƴanbidigar kusan 200 ciki har da manyan kwamandojin Bello Turji. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyin jama'a mabanbanta...
-
Kan tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila
25/06/2025 Duration: 09minShirin na yau ya baku damar tofa albarkacin bakinku game da tsagita wuta da aka yi tsakanin Iran da Isra'ila bayan kwashe kusan kwanaki 12 ana gwabza yaƙi. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.