Kasuwanci

Dalilan da suka sanya farfaɗowar darajar Naira a kasuwar musaya

Informações:

Synopsis

Shirin ‘Kasuwa a kai miki Dole’ tare da Nura Ado Suleiman ya tattauna kan farfaɗowar darajar Naira a kasuwar hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare, musamman ma a kan Dalar Amurka, nasarar da wasu ke ganin ta biyo bayan manufofin da babban bankin Najeriya CBN ke aiwatarwa. Bayanai dai sun nuna cewa darajar Naira na ta ƙaruwa ne kusan a kowace rana tun daga watan Janairun wannan shekara da mu ke ciki ta 2025. Nasarar da wasu Magidanta suka ce sun shaida samun ta, la’akari da sauƙin da aka fara samu a harkokinsu na yau da kullum.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....