Ilimi Hasken Rayuwa

Yadda tsadar lantarki ke kassara harkokin karatun manyan makarantun Najeriya

Informações:

Synopsis

A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya.Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki. To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a kusan manyan makarantun Najeriya, wata matsalar kuma ita ce ta tsadar wutar a sakamakon ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ta yi.Wannan dalili ne ya sanya ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya, ta yi kashedin cewa jami’o’in tarayyar ƙasar aƙalla 52 ka iya durƙushewa nan ba da jimawa ba, a sakamakon tsadar kuɗin wutar.Shugabannin Jami’o’in na Najeriya, sun yi wannan gargaɗi ne bayan wani sabon ƙari na kashi 300 da aka yi musu a kwanakin baya.Kuna iya latsa alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...