Synopsis
Wannan Shirin na Kida da Al'adu ana gabatar da shi ne a Karshen mako domin shakatar da masu saurare.
Episodes
-
Yadda Hausawa ke tafiyar da masarautarsu a Jihar Edo
07/05/2024 Duration: 10minShirin na wannan mako zai yi duba ne kan yadda Hausawa ke tafiyar da masarutar su a yankin Edo wato jihar Benin a tarayyar Najeriya Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa
-
Nafisa Abdullahi da Sarkin Waka sun janyo cece-ku-ce a Kannywood
30/04/2022 Duration: 20minShirin wannan mako ya zagaya masana'antun fina finai dabam dabam, inda a Kannywood, wato masana'antar fina finan Hausa ta Najeriya ya kawo labarin yadda kalaman da jaruma Nafisa Abdullahi ta y a kan 'yayan da ake haifa ba a san yadda za a yi da su ba' ya janyo cece kuce, bayan da Naziru Sarkin Waka ya yi mata raddi.
-
Halin da mawakiya Oumou Sangaré ke ciki
24/04/2022 Duration: 19minShirin Finafinai kadekade da Al'adu, ya dauko muku kadan daga cikin abubuwan da suka faru a KANNYWOOD.Mun kuma Tattauna da mawaki MUKTAR BANDANA game da wakar (Ramadana yana ban kwana). Sai kuma bangaren Al'adu tare daTauraruwar waka OUMOU SANGARE wacce zata saki sabon album mai suna Timbuktu ranar 29 ga wata na Afrilu bayan ta dau lokaci bata saki wata wakarba tun bayan shekarar 2017."
-
-
Shagulgulan Biyanu wata al’adar da mutan Agadez ke rayawa shekaru aru aru
24/09/2019 Duration: 10minA shirin namu na yau zai yada zango ne a jihar Agadez dake arewacin jamhuriyar Nijar domin duba shagulgulan biyanu wata al’adar da mutan Agadez ke rayawa shekaru aru aru da suka gabata da ake kira Biyanu.Muhammed Billal mai mukamin Agolla daya daga cikin masu shirya Biyanun ya samu zantawa da rediyon Faransa rfi.
-
-
Shahararren mawakin Najeriya Mamman shata ya cika shekaru 20 da barin duniya
02/07/2019 Duration: 10minShirin Kida da al'adun gargajiya tare da Mahaman Salissou Hamissou a wannan makon ya dora akan inda shirin ya tsaya a makon jiya, game da yadda Mamman Shata Katsina ya cika shekaru 20 da barin duniya dama tasirin wakokinsa ga bunkasuwar harshen hausa.
-
shagulgulan Sallar Idil Fitr a Najeriya
15/06/2018 Duration: 20minA Najeriya Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci karkashin jagorancin mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ita ce ta tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a jihohi da dama na kasar a yammacin jiya.Ko baya ga Najeriya, a yau ana gudanar da bukukuwan sallar a mafi yawan kasashen muslumi da suka hada da Chadi, Kamaru, Ghana, Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larawaba da dai sauransu.
-
shagulgulan Sallar azumin Ramadana a Nijar
15/06/2018 Duration: 20minAl’ummar musulmi a sassa da dama na duniya na gudanar da bukukuwan karamar sallah wato Idil Fitr a yau juma’a, bayan kammala azumin watan Ramadana.A Najeriya Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci karkashin jagorancin mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ita ce ta tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a jihohi da dama na kasar a yammacin jiya.A cikin shirin na musaman Abdoulaye Issa ya duba wasu daga cikin muhiman batutuwa da jama'a suka mayar da hankali a kai a Nijar.
-
Aure a duniyar hausa
14/11/2017 Duration: 10minA cikin shirin al'adu na gado Salissou Hamissou ya duba yanayin aure a duniyar hausa.Za ku ji irin sauyi da aka samu,dama yadda mutane ke kallon halin da ake ciki.
-
Tattaunawa da Rogazo mawakin gargajiyar Nijar
15/03/2016 Duration: 10minMawakin Gargajiya da ake kira Rogazo dai ya shahara wajen yin fira cikin wake, ya kuma gwada irin basirar da Allah ya yi masa a zantawa da Mahaman Salissou Hamisou
-
Kida da Al'adun Nufawa a Najeriya
23/01/2016 Duration: 19minHaoua Kabir cikin shirin al'adun mun na gado ta duba mana yadda yan kabilar Nufawa ke rayyuwa dama zamantakewa .
-
Kida da Al'adun Nufawa
09/01/2016 Duration: 20minShirin Kida da Al'adu ya tattauna da Mawakiyar Nufawa Amina Ibrahim da ake kira Kashekala sannan shirin ya diba wasu al'adun Nufawa.
-
Mawakin Yanayi: Lawal Musa Dankwari
12/12/2015 Duration: 19minShirin Kida da Al'adu ya tattauna da Lawal Musa Dankwari Malamin Hausa a Zaria wanda ya rera wake kan sauyin yanayi da ake samu a yanzu da tsabtace muhalli. Dankwari ya wake Ruwa da Daji da tsirrai da tsunsaye.
-
Yadda Hausawa ke aure kafin zuwan musulunci
21/11/2015 Duration: 19minShirin Kade-kade da Al'adu na wannan karo tare da Hauwa Kabir, ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke aure kafin zuwan musulunci.
-
Shahrarrun mawakan Mali, makafi Amadou da Mariama
14/11/2015 Duration: 19minShirin ''Kida da Al'adu'' tare da Hauwa Kabir, a wannan mako ya duba rayuwar shahrarrun mawakan kasar Mali Amadou da Mariama, mata da miji kuma makafi da suka yi fice sosai a fagen waka.
-
Labarin shahrarrun makada da mawaka, tare da karin bayani game da al'adun wasu al'ummomi
31/10/2015 Duration: 20minKade-kade da Al'adu tare da Hauwa Kabir, shiri ne da ke ba ku labarun shahrarrun makada da mawaka tare da yin dubi a game da al'adun wasu al'ummomi.
-
Ma'anar hawa da Sarakunan Hausa ke yi lokacin bukukuwa
25/10/2015 Duration: 20minShirin Kade-kade da Al'adu a wannan karo, Hauwa Kabrir ta yi dubi ne a game da ''Hawa'' da sarakuna ke yi a kasar Hausa, a lokacin gudanar da bukukuwa.
-
Shirin kade-kade da al'adu na karshen mako
17/10/2015 Duration: 20minA sha saurare lafiya tareda Hauwa Kabir
-