Synopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodes
-
Alhaji Muhammadu Magaji kan saye kayan amfanin gona a Najeriya
13/11/2024 Duration: 03minMazauna yankin arewacin Najeriya na bayyana damuwa kan yadda kamfanoni da ƴan kasuwa ke rige rigen sayen kayan abinci a hannun manoma. Masana na bayyana fargabar cewar matakin zai sanya kayan abincin ya yi tsada a daidai lokacin da jama'a ke fama da tsadar rayuwa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Muhammadu Magaji, Sakataren tsare tsare na ƙungiyar manoman Najeriya dangane saye kayan abincin. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar ta su........
-
Tattaunawa da Abdullahi Idris Zuru kan harin Lakurawa a jihar Kebbi
11/11/2024 Duration: 03minSabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa da ta bayyana a makwannin baya-bayan nan cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya ta hallaka aƙalla mutane 15 a harin da ta kai garin Mera na jihar Kebbi baya ga kora tarin dabbobin jama’a.Bayanai sun ce an yi artabu tasakanin yan ta’addan da mutanen gari gabanin tserewarsu. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kakakin gwamnatin jihar kebbi Abdullahi Idris Zuru wanda ya bayyana cewa tuni gwamnati ta ɗauki matakan baiwa jama'a kariya baya ga aikewa da twaga don bin sahun ƴan ta'addan.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Farfesa Bello Bada kan bullar sabuwar kungiyar ta'addanci a Najeriya
08/11/2024 Duration: 03minRundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da samun wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ake kira Lakurawa a Jihohin Sokoto da Kebbi wadanda aka ce sun fito ne daga kasashen mali da Libya da kuma Jamhuriyar Nijar. Rahotanni sun ce 'yayan wanan kungiya na sanya haraji da kafa dokoki a yankunan da suke.Dangane da wannan sabon al'amari, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Sule Ammani kan abin da ya biyo bayan nasarar ƙubutar da yaran arewacin Najeriya
06/11/2024 Duration: 03minGa dukkan alamu matsalar da ta biyo bayan kama ƙananan yaran da ƴan sandan Najeriya su ka yi lokacin zanga-zangar tsaɗar rayuwa a Kano ta zaburar da wasu daga cikin shugabannin yankin kan bukatar haɗa kai domin ceto arewacin ƙasar daga halin da ya samu kansa, bayan sakin yaran, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ɗaya daga cikin dattawan yankin Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina.
-
Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan tasirin zaɓen Amurka ga Duniya
05/11/2024 Duration: 03minYau Amurkawa ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasar da bayanai ke cewa fiye da mutum miliyan 180 za su jefa ƙuri'unsu don zaɓen guda cikin ƴan takara biyu da ke fafatawa wato tsohon shugaban ƙasar Donald Trump na jam'iyyar Republican da Kamala Harris ta Jam'iyyar Democrat wadda mataimakiyar shugaban ƙasa ce kuma ƴar takarar mace baƙar fata ta farko a tarihin ƙasar. Domin jin tasirin wannan zaɓe da ya ɗauki hankalin duniya Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze.
-
Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan tasirin zaɓen Amurka ga Duniya
05/11/2024 Duration: 03minYau Amurkawa ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasar da bayanai ke cewa fiye da mutum miliyan 180 za su jefa ƙuri'unsu don zaɓen guda cikin ƴan takara biyu da ke fafatawa wato tsohon shugaban ƙasar Donald Trump na jam'iyyar Republican da Kamala Harris ta Jam'iyyar Democrat wadda mataimakiyar shugaban ƙasa ce kuma ƴar takarar mace baƙar fata ta farko a tarihin ƙasar. Domin jin tasirin wannan zaɓe da ya ɗauki hankalin duniya Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze.
-
Attahiru Bafarawa kan tsare yaran arewacin Najeriya saboda zanga zanga
04/11/2024 Duration: 03minƘungiyar Amnesty International a Najeriya tare da wasu ƙungiyoyin kare hakkin Bil Adama da kuma wasu fitattun ƴan ƙasar sun bayyana damuwa dangane da yadda rundunar ƴan sandan ƙasar ta gurfanar da wasu yaran da suka fita hayyacinsu a gaban kotu, inda ake tuhumarsu da zanga zangar neman kifar da gwamnati. Rahotanni sun ce ministan shari’a ya bukaci mika masa takardun shari’ar wadda ta haifar da cece kuce a fadin ƙasar. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ɗaya daga cikin dattawan arewacin Najeriya, kuma tsohon Gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.
-
Halin da masana'antun arewacin Najeriya ke ciki na rashin wutan lantarki
31/10/2024 Duration: 03minMasu masana'antu a arewacin Najeriya sun bi sahun sauran jama'ar yankin wajen bayyana damuwarsu a kan halin da suka samu kansu na rashin wutan lantarki sama da kwanaki goma. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mataimakin shugaban ƙungiyar masu masana'antu ta ƙasa MAN, Ali Safiyanu Madugu.
-
Farfesa Shehu Abdullahi Zuru game da binciken wasu alkalai a jihar Rivers
30/10/2024 Duration: 03minBabbar mai shari'a a Najeriya tare da Hukumar Kula da Ayyukan Shari'a ta NJC sun kaddamar da bincike a kan yadda wasu alkalai a jihar Rivers suka dinga bada hukunce hukunce da ke karo da juna dangane da zaben kananan hukumomin da aka yi a jihar. Wannan umarni na zuwa ne bayan an samu irin wannan matsala a jihar Kano. Saboda haka Bashir Ibrahim Idris ya tintibe masanin ɓangaren shari'a Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na jami'ar Baze dake Abuja. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.........
-
Murtala Aliyu kan matsayar ACF na rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya
29/10/2024 Duration: 03minƘungiyar Tintiba ta Arewacin Najeriya da ake kira ACF, ta bi sahun wasu jama'ar yankin wajen bayyana damuwarta kan matsalar rashin wutar da ake fuskanta na sama da mako guda a yankin, inda ta buƙaci shugaban ƙasar da ya kafa dokar ta ɓaci a kan lamarin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren kungiyar, Malam Murtala Aliyu, wanda tsohon ministan wutar lantarki ne a ƙasar Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana........
-
Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina kan rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya
28/10/2024 Duration: 03minMazauna yankin Arewacin Najeriya sun kwashe kwanaki 7 ba tare da hasken wutar lantarki ba, abinda ya yi sanadiyar durkushewar jama'a musamman masu sana'oin da suka dogara ga wutar. Wannan matsala na barazana ga rayuwa da kuma tattalin arzikin yankin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daya daga cikin dattawan yankin, Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawarsu ta su........
-
Dokta Abbati Baƙo kan taron BRICS da ake yi a Rasha
24/10/2024 Duration: 03minShugaban Rasha Vladimir Putin ya ce taron kasashen BRICS dake gudana a kasarsa zai duba yiwuwar samar da wata sabuwar tafiya wadda za ta yi gogaggaya da wadda ake amfani da ita a duniya yanzu haka.Akalla shugabannin kasashe 30 ke halartar taron a birnin Kazan.Domin tasirin wannan kungiya ta BRICS dake Shirin kawo sauyi a duniya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Bako masanin siyasar duniya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Dr Yahuza Ahmad Getso kan fargabar kwararar ƴan ta'adda zuwa jihar Kano
22/10/2024 Duration: 03minWani sabon rahoton binciken kwakwaf da aka gudanar ya bankado yadda ‘yan ta’adda daga jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina da kuma Kaduna ke tsallakawa jihar Kano domin samun mafaka. Jihar Kano ce dai ke da dama-dama ta fannin ingancin tsaro a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.Shin yaya masana ke kallon wannan sabon salo da kuma hatsarin da yake da shi, Rukayya Abba Kabara ta tattauna da Dr Yahuza Ahmad Getso masanin tsrao a Najeriya, ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar......
-
Dr Kasum Garba Kurfi game da yabawa tsarin tattalin arzkin Najeriya da bankin duniya yayi
21/10/2024 Duration: 03minBankin duniya ya yaba da sauye sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriya ke aiwatarwa, tare da bai wa hukumomin ƙasar shawarar kar su kuskura su koma da baya. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da talakawan ƙasar ke kokawa saboda ƙuncin rayuwa. Dangane da wannan matsayi Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dr Kasum Garba Kurfi. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawarsu..............
-
Sojojin Nijar sun gaza a yaƙi da rashawa - Transparency International
18/10/2024 Duration: 03minƘungiyar Transparency International da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, reshen Jamhuriyar Nijar ta fitar da wani sabon rahotoda ke zargin sojojin ƙasar da gazawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma hana fararen hula guraben shugabancin hukumomin gwamnati. Dangane da wannan zargi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban Transparency International, reshan Nijar, Mamman Wada.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
-
Kaften Isa Usman: Halin da shugaba Paul Biya na Kamaru ke ciki
11/10/2024 Duration: 03minYayin da tababa da rashin tabbas suka mamaye halin da shuhgaban Kamaru Paul Biya ke ciki, gwamnatin ƙasar ta haramta wa kafofin yaɗa labarai sharhi dangane da shugaban. A kan wannan batu ne, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kaften Isa Usman, tsohon dogarin Ahmadou Ahidjou da kuma shi kansa Paul Biya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
-
Comrade Umar Danjani Hadejiya kan ƙara kuɗin man fetur a Najeriya
10/10/2024 Duration: 03minA karo na 4 tun bayan hawa karagar mulkin shugabancin Najeriya da Bola Ahmed Tinubu yayi, kamfanin man NNPCL ke sanar da ƙara farashin man fetur, inda yanzu farashin ya koma naira 998 a Lagos, ya yin da Abuja kuma ya koma naira dubu 1 da naira 30. Wannan ya sa talakawan ƙasar sake gabatar da korafinsu saboda yadda farashin zai sake shafar kayan masarufi. Dangane da wannan sake karin, Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da Comrade Umar Danjani Hadejiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu......
-
Prof Shehu Abdullahi Zuru kan binciken yadda ƴan Afrika basa jin daɗin mulkin dimukaradiya
09/10/2024 Duration: 03minShugaban Gidauniyar Shehu Musa Yar Adua Akin Kekere-Ekun, ya bayyana cewar kashi 80 na jama'ar nahiyar Afirka ba sa jin daɗin yadda zaɓaɓɓun shugabanninsu ke tafiyar da mulkin dimukiraɗiya a ƙasashen su. Jami'in ya ce akwai wagegen giɓi tsakanin yadda shugabannin ke mulki da kuma buƙatun jama'a, musamman abinda ya shafi ayyukan da suke so. Dangane da binciken da Gidauniyar ta yi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze da ke Abuja. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Sama'ila Mohammed kan ɗauki-ɗora a zaɓen ƙananan hukumomi a Najeriya
08/10/2024 Duration: 03minGa alama yunkurin tabbatar da dimokiradiya a yankunan kananan hukumomin Najeriya da kuma sake musu mara domin cin gashin kansu na ci gaba da fuskantar kalubale, ganin yadda zabukan kananan hukumomi suka zama dauki dora, inda jam'iyyar gwamnan da ke mulkin jiha ke lashe daukacin kujerun kananan hukumomin jihar. Domin sanin inda matsalar ta ke da illar da za ta yi wa dimokiradiya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Samaila Muhammed, tsohon shugaban karamar hukumar Jos dake Jihar Filato, kuma tsohon dan majalisar tarraya. Ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Dr Elharun Muhammed kan cika shekara ɗaya da faro yakin Hamas da Isra'ila
07/10/2024 Duration: 03minYau ake cika shekara guda da kazamin harin da mayakan Hamas suka kai wa Isra'ila wanda ya yi sanadiyar barkewan yakin da ya lakume rayukan mutane sama da dubu 45 daga bangarorin biyu. Duk wani ƙoƙarin sasanta rikicin ya gagara, yayin da yakin ke ci gaba da fadada. Dangane da halin da ake ciki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Elharun Muhammed, mai Cibiyar kula da manufofin ƙasashe da kuma ci gabansu. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.......