Synopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodes
-
Abubakar Abdullahi mai ritaya kan zanga-zangar tsoffin 'yan sandan Najeriya
22/07/2025 Duration: 03minA ranar Litinin ne tsofaffin 'Yan Sandan Najeriya da suka yi ritaya suka gudanar da zanga-zanga a biranen ƙasar da kuma Abuja, saboda gabatar da ƙorafi akan yadda ake biyan su fansho da kuma neman fitar da su daga tsarin da ake amfani da shi yanzu haka. Bayan kammala zanga zangar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da CSP Abubakar Abdullahi dashe mai ritaya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
An ɗauki hanyar samun zaman lafiya a Jamhuriyar dimokaraɗiyar Congo
21/07/2025 Duration: 03minAn fara samun haske a game da kawo ƙarshen rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda a ranar Asabar makon da ya gabata a birnin Doha na Qatar ƙasar, da kungiyar yan tawayen M23 suka rattaba hannu akan wata yarjejeniyar tsagaita wuta da zumar kawo ƙarshen yakin da suke yi a tsakaninsu. A cikin yarjejeniyar, dukkannin bangarorin sun amince su tsagaita kai wa juna hare-hare tare da dakatar da farfagandar nuna ƙiyayya. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Dokta Abbati Bako, masanin dangantakar ƙasa da ƙasa daga jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya.
-
Hira da Kwamared Umar Hamisu Ƙofar Na’isa kan matakin ladabtar da yansanda
17/07/2025 Duration: 03minKamar yadda akaji a farkon Shirin, Hukumar kula da ƴansanda a Najeriya ta gurfanar da manyan jami’ai sama da 150 a gaban kwamitin ladabtarwa, bisa zarginsu da wulakanta aikin ɗansanda da kuma take hakkoki fararen hula a wasu lokutan. Bayanai sun ce an baiwa kwamitin kwanaki 10 ya gama binciken ƴansanda masu muƙamin ASP zuwa sama, ya kuma gabatar da rahoto wanda zai baiwa hukumomi damar ɗaukar matakin hukunci a kansu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiya hirar.....
-
Tattaunawa da Isma'ila Muhammed ɗan siyasa a Kamaru game da takarar Paul Biya
15/07/2025 Duration: 03minShugaba Paul Biya na Kamaru mai shekaru 92 ya bayyana aniyar sake tsayawa takara don neman wa'adi na 8 na mulkin ƙasar da nufin ci gaba da yiwa ƙasar hidima. Shugaba Biya ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta. Sai dai ko yaya jama'ar Kamaru ke kallon wannan mataki, dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Isma'ila Muhammed ɗan siyasa a ƙasar ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..