Synopsis
Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.
Episodes
-
Taba Ka Lashe: 15.01.2025
21/01/2025 Duration: 09minShekaru aru-aru maroka da mawakan baka na bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen bunkasa al'adu da martaba kimar al'umma a daular Hausa.
-
-
Taba Ka Lashe: 01.01.2025
07/01/2025 Duration: 09minKo kun san cewa har yanzu ana gudanar da al-adar nan ta sayen baki a Kasar Hausa idan an yi aure? Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
-
Taba Ka Lashe: 04.12.2024
10/12/2024 Duration: 09minTsarin karatun Allo na neman ilimin da gwamnatin jihar Borno a Najeriya ke kokarin kyautatawa
-
Taba Ka Lashe 03.12.2024
03/12/2024 Duration: 09minShirin na al'adu ya duba tasirin gidan tarihi na Arewa (Arewa House) da ke Kaduna da ya tattara tarihin Marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da al'adu da sana'o'in yankin Arewacin Najeriya.
-
Taba Ka Lashe 20.11.2024
26/11/2024 Duration: 10minShirin ya duba al'adar kacici-kacici ko wasa kwakwalwa da malam Bahaushe ke amfani da ita wajen ilimantawa.
-
Taba Ka Lashe: 07.11.2024
12/11/2024 Duration: 09minShirin ya mayar da hankali ne kan masarautar Wurkun da ke karamar hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba da ke tarayyar Najeriya,
-
Taba Ka Lashe 06.11.2024
06/11/2024 Duration: 09minShirin ya duba al'adar Masquerade, ko Basaje kamar yadda ake fassarawa, da ta kafu a yankin Kabilar Igbo a Najeriya.
-
Taba Ka Lashe 29.10.2024
29/10/2024 Duration: 09minShirin ya duba fadi tashin da kungiyar Fudeco ke yi don ceto al'adun Fulani tare tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu da sauran al'umma
-
Taba Ka Lashe 09.10.2024
09/10/2024 Duration: 09minShirin ya duba takaddamar da ta barke a bikin cika shekaru 75 da fara bikin bajekolin litattafai na birnin Frankfurt na Jamus.
-
Taba Ka Lashe: 25.09.2024
01/10/2024 Duration: 09minAl'adar shan barasa na shekara-shekara a birnin Munich na Jamus
-
Taba Ka Lashe 24.09.2024
24/09/2024 Duration: 09minShirin ya duba yadda wakokin baka ke kasance kamar wani tubali na gina al’umma, wanda ta hanyarsa ne ake samun ilimi, tarbiyya da kuma bunkasar tattalin arziki.
-
Taba Ka Lashe: 11.09.2024
17/09/2024 Duration: 10minShigowar zamani na neman kawar da maroka da sankira
-
Taba Ka Lashe. 03.09.2024
10/09/2024 Duration: 09minGuda: Wata al'ada ce da ake yi ga sarakuna da kuma amare da angwaye yayin bukukuwa a Kasar Hausa. Ko kun san tasirin guda ga angwaye da ma amare? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 14.08.2024
20/08/2024 Duration: 09minSha'irai mawakan Manzon Allah da Ahlil baitin gidansa da kuma waliyyai na karuwa a tsakanin matasa a Jamhuriyar Nijar.
-
Taba Ka Lashe: 13.08.2024
13/08/2024 Duration: 09minShirin ya duba yadda 'yan Afirka ke gudanaar da addinansu da ibadansu a kasar Jamus inda suke da zama. Wai shin suna zuwa masallantai da majami'u?
-
Taba Ka Lashe: 31.07.2024
06/08/2024 Duration: 09minKo kun san cewa akwai wasu tarin kabilu a jihar Kaduna da ke Tarayyar Najeriya, wadanda suka alkinta wasanni da al'adunsu? Shirin Taba Ka Lashe ya tattauna da su.
-
Taba Ka Lashe 18.07.2024
18/07/2024 Duration: 09minShirin ya duba busa algaita da ake yi a lokacin taron sarakuna ko biki ko wata haduwa a tsakanin Barebari ko Kanuri .
-
Taba Ka Lashe: 10.07.2024
16/07/2024 Duration: 09minWani wuri a Zuru da ke jahar Kebbi ana kiransa da suna (Girmace), a wannan wuri ne da mutane ke rayuwa tare da Kadoji.
-
Taba Ka Lashe: 03.07.2024
09/07/2024 Duration: 10minMasarautun gargajiya na zama tushen shugabanci da jagorancin al'ummar arewacin Najeriya, wanda ko a zamanin Turawan mulkin mallaka an ga yadda suka tafi tare da su. Sarakuna kan zamo alkiblar al'umma ta fuskar gudanar da rayuwa da dukkan al'amura na yau da kullum, kama daga harkokin neman ilimi da kasuwanci da zamantakewa da sana'o'i da dukkan lamuran da suka shafi al'adu da ma addinai.