Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu saurare kan shigar iyayen al'umma cikin ayyukan garkuwa da mutane

Informações:

Synopsis

Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya duba yadda rashin tsrao da kuma garkuwa da mutane ke kara yawaita a arewacin Najeriya, inda a baya-bayan nan kwamishin yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ya sanar da cafke 'dan majalisar dokoki da hakimi tare da tsohon shugaban karamar hukumar Kaurar Namoda bisa zarginsu da hannu dumu dumu cikin ayyukan garkuwa da mutane domin karbar kuɗin fansa. Wannan al’amari ya sake tabbatar da zargin da ake yi wa wasu daga cikin shugabanni a Najeriya dangane da taka muhimmiyar rawa a matsalolin tsaron da suka addabi al’ummar ƙasar.Me za ku ce kan wannan lamari?Wane darasi ya kamata al’umma su koya?Wace mafita ce mafi dacewa a bi wajen magance matsalolin tsaron dake tagayyara jama’a?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare da Nasiruddeen Muhammad