Lafiya Jari Ce

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:59:17
  • More information

Informações:

Synopsis

Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.

Episodes

  • Tiyatar fitar da jarirai daga cikin Uwa na yawaita a sassan Najeriya

    24/02/2025 Duration: 10min

    Shirin Lafiya jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda fasahar cire ɗa ta hanyar CS ke taimakawa wajen ceto rayukan uwa da ɗa da nufin rage asarar rayukan da ake fuskanta a lokacin haihuwa. Duk da cewa haihuwa 3 cikin 100 ce kaɗai ake yi ta hanyar tiyata ko kuma CS a Najeriya bisa alƙaluman 2019, amma a baya-bayan nan ana ganin yawaitar matan da ake yiwa CS gabanin haihuwa kama daga nau'in matan da basa zuwa asibiti da kuma mata masu shekaru da yawa ko waɗanda suka yi haihuwa da dama, duk dai a ƙoƙarin kange yawaitar mace-macen mata ko kuma asarar jariran da ake gani a sassan ƙasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

  • Mahukuntan Najeriya sun tsawaita shekarun aiki ga likitoci da jami'an lafiya

    17/02/2025 Duration: 09min

    Shirin ''Lafiya Jari Ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya na tsawaita lokacin ritayar likitoci da malaman jinya a wani yunƙuri na ganin sun ci gaba da bayar da gudunmawa ga al’ummar wannan ƙasa wadda ke fama da ƙarancin ƙwararrun likitoci. Matakin na gwamnatin Najeriya ya nuna cewa Likitocin ko kuma sauran jami’an lafiya na da zaɓin ƙarin shekaru 5 akan ainahin shekarunsu na ritaya, ta yadda za su kai har shekaru 65 na haihuwa a bakin aiki maimakon shekaru 60 a baya, ko da ya ke wannan mataki bai samu maraba daga wasu unguzoma ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....

  • Lafiya Jari Ce: Illar rashin zuwa awon ciki ga lafiyar mata da jariransu

    10/02/2025 Duration: 10min

    Shirin ''Lafiya Jari ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matsalar rashin zuwa awo da ke matsayin babban ƙalubalen ga mata masu juna biyu a yayin goyon ciki ko kuma haihuwa, matsalar da aka fi ganin ta’azzararta a yankunan karkara, wadda a lokuta da dama ke kaiwa ga asarar rayukan walau uwa ko jariri. Ƙorafe-ƙorafen jami’an lafiya na ci gaba da yawaita kan matsalolin da suka dabaibaye tsarin renon ciki da kuma haihuwa a yankunan karkara, matsalar da wala’alla ake ganin ta na da alaƙa ta ƙut da ƙut da halin matsi ko kuma tsadar rayuwar da ake fama da ita wadda ta ƙai ƙololuwa a yankin arewacin Najeriya mai fama da durƙushewar ɓangaren kiwon lafiya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

  • Barazanar da fannin lafiya ke fuskanta kan ficewar likitoci daga Najeriya

    27/01/2025 Duration: 10min

    Shirin lafiya Jari ce na wannan makon ya taɓo batun yadda kwararrun likitoci ke tserewa daga Najeriya, inda wasu alkaluma suka nuna cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, sama da likitoci dubu 16 suka fice daga ƙasar don yin aiki a wasu ƙasashen ketare, lamarin da ke barazana ga tsarin kula da lafiya a ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............

page 2 from 2