Wasanni

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:58:44
  • More information

Informações:

Synopsis

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Episodes

  • Sharhi kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da PSG ta lashe

    02/06/2025 Duration: 10min

    Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya yi duba ne kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da aka yi a ƙarshen mako tsakanin PSG ta Faransa da kuma Inter Milan, inda PSG ta samu nasarar lashe gasar bayan da ta zazzaga wa Inter Milan ƙwallaye biyar. Wannan ne dai karon farko da PSG ta lashe wannan kofi, kuma karo na farko da wata ƙungiya daga Faransa ta lashe shi tun bayan Marseille a shekarar 1993.Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Khamis Saleh............

  • Yadda bukin wasanni na ƙasa ke gudana a Abeokutan Najeriya

    26/05/2025 Duration: 10min

    Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon tare da Khamis Saleh yi yi dubi ne kan bikin wasannin na ƙasa da ke gudana a jihar Ogun da ke Najeriya.

  • Dalilan durkushewar ƙungiyoyin Arewacin Najeriya da suka bada gudunmuwa a baya - Kashi na 3

    19/05/2025 Duration: 09min

    A wannan makon shirin zai ɗora ne akan wanda muka kawo a baya, wanda ya yi bita a game da wasu shahararun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na arewacin Najeriya da suka taimaka wajen ƙyanƙyasar fitattun ƴan wasa da suka yi shura a fagen ƙwallon ƙafa a ƙasar. Shirin ya yaɗa zango ne a Kano, inda ya gana da wasu tsaffin fitattun ƴan wasa, musamman na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Racca Rovers.

  • Dalilan durkushewar ƙungiyoyin Arewacin Najeriya da suka bada gudunmuwa a baya - Kashi na 2

    12/05/2025 Duration: 10min

    A wannan makon, shirin Duniyar Wasanni ya ɗora ne kan shirin mu daya gabata, wanda yayi duba kan yadda manyan ƙungiyoyin da suka taimakawa Najeriya wajen ƙyanƙyansar shahararrun ƴan wasa daga yankin Arewacin ƙasar suka durkushe. A wannan makon shirin zai yada zango ne a garin Jos na jihar Filato, wanda ke zama gida ga ƙungiyar Mighty Jets FC. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........

page 2 from 2