Synopsis
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episodes
-
Tasirin naɗin da wasu Masarautu ke yiwa waɗanda ba ƙabilunsu ba
18/02/2025 Duration: 10minShirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan al'adar nan ta naɗin sarauta da wasu masarautun gargajiya ke yi ga ƙabilun da ba su ke da masarautar ba, wanda hakan ya biyo bayan sabbin naɗe-naɗe da ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙabilar gwari a arewacin Najeriya ta yi wa wasu manyan shuwagabannin al'ummar fulani a jihar Neja. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun masarautun Hausa da Fulani da ma wasu masarautun a yankin kudanci da kuma arewacin Najeriya ke baiwa ƙabilun da ke zaune a masarautar sarauta ba, abin da shirin Al'adu na wannan mako ya yi nazari akai tare da jin inda hakan ya samo asali da kuma alaƙar da ke tsakanin al'adun ƙabilar gwari da fulani daga masana al'adu da masarautu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
-
Yadda tsamin alaƙar gwamnati da Sarakuna ke raunata Masarautun gargajiya
11/02/2025 Duration: 09minShirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi. A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al’adu ke kallon al’amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Yadda al'ummar ƙasar Hausa suka rungumi al'adar shaƙe a matsayin magani
04/02/2025 Duration: 10minShirin Al’adunmu na gado na yau, ya yi duba ne kan al’adar shaƙe a ƙasar hausa da wasu kan yi a matsayin al’ada da kuma magani. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Ƴan China da ke Najeriya sun gudanar da bikin sabuwar shekararsu
28/01/2025 Duration: 09minShirin Al’adun mu na gado na wannan makon ya mayar da hankali ne ga bukuwan sabuwwar shekara na ƴan ƙasar China, bukukuwan da aka gudanar a sassa daban daban na duniyar. A Najeriya, ƴan China ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da wannan biki a biranen Abuja da kuma Lagas, wanda ya samu halarta jama’a baki daga ciki da waje. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........