Synopsis
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episodes
-
Najeriya ta yi asarar sama da naira triliyan 5 a zanga-zangar kwanaki 10
14/08/2024 Duration: 09minShirin Kasuwa A kai miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya tattauna irin asarar da aka yi a Najeriya sakamakon zanga zangar kwanaki 10 da ƴan ƙasar suka yi domin nuna adawa da tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari. Ministar masana’antu da Kasuwanci da kuma zuba jari na kasar Dr. Doris Uzoka Anite ta ce, alkakuma da suka tattara na wucin gadi, sun nuna cewa Najeriya ta yi asarar naira biliyan 500 a duk rana ta Allah yayin zanga-zangar, bayaga dukiyar da aka barnata ta hanyar kone-kone ko sata da makamanci hakan da takai naira biliyan 52, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
-
Yadda basuka su ka yi wa ƙasar Ghana katutu a cikin shekara guda
07/08/2024 Duration: 09minA yau shirin zai waiwai kasar Ghana, inda basusukan da ake bin kasar ya karu da dala biliyan 47.4 / Cidi biliyan 658.6 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2024.Babban Bankin ƙasar ta Ghana ne ya fitar da wadandan alkaluma cikin wani rahoton da ya fitar na taƙaitaccen Bayanan Tattalin Arziki da Kuɗi na watan Mayun shekarar 2024. A cewar babban bankin na Ghana, bashin da ake bin ƙasar ya karu ne zuwa Cidi biliyan 658.6 a watan Fabrairun wannan shekarar, tsabanin Cidi biliyan 611.2 da yake a ƙarshen shekarar 2023.
-
Yadda Najeriya ke fuskantar tashin farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 30
24/07/2024 Duration: 10minA wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al’umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata. Shin ko hakan zai kawo sauƙi kan halin da ake ciki a ƙasar? Kuna iya latsa alamar sauti don jin amsar wannan tambaya tare da masana ta cikin shirin...