Lafiya Jari Ce

Muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zallah a watannin shidan farko

Informações:

Synopsis

  A wannan makon shirin ya yi duba kan tsarin nan na shayar da nonon uwa zalla ga jarirai tun daga haihuwa har zuwa watanni 6 ba tare da silki ba, tsarin da ake cigaba da ganin mabanbantan ra’ayoyi hatta daga iyaye dama wasu jami’an lafiya. Bisa al’ada kowanne makon farko na watan Agusta na matsayin makon shayar da Nonon uwa zalla da ake kira Exclusive Breast Feeding a turance, da nufin ƙarfafa gwiwar iyaye wajen rungumar tsarin na shayar da Nonon Uwa zalla ga jarirai, makon da a wannan shekarar ke da taken Fifita tsarin shayar da jarirai Nono zalla don samar tallafi mai ɗorewa.