Bakonmu A Yau

Tattaunawa da masani Umar Saleh Anka kan ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya 30

Informações:

Synopsis

Gwamnatin Najeriya ta yi gargaɗin cewa jihohi 30 na ƙasar na fuskantar barazanar iftila’in ambaliyar ruwa yayin da daminar bana ta soma, kuma tuni ta fara shirin ƙaddamar da gangamin wayar da kan mutane game da illar ta da kuma hanyoyin rage kaifinta. To ko wace rawa hukumomi da al’umma za su taka dangane da rage mummanar illar da ambaliyar ke yi?Hauwa Halliru Gwangwazo ta tattauna da Umar Saleh Anka na ƙungiyar rajin kare muhalli a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar