Lafiya Jari Ce

Lafiya Jari ce: Illar da hayaƙin girki ke yiwa lafiyar idon Mata

Informações:

Synopsis

A wannan makon shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani gargaɗin masana game da illar hayaƙi ga lafiyar jama’a a wani yanayi da masanan ke ganin mazauna garuruwa irin Kano da Sokoto da Kwara baya ga kaso mai yawa na jihohin arewacin Najeriya na cikin haɗarin kamuwa da cutukan masu alaƙa da numfashi sakamakon yadda suka dogara da itace ko kuma gawayi wajen yin girki. A ɓangare guda wasu ƙwararrun na ganin matan da suka shafe lokaci suna girki da itace ka iya fuskantar matsalar ido, tambayar a nan ita ce ko matan na da masaniya kan illar hayakin girki ga lafiyar idonsu? Ku biyo mu a cikin shirin don sauraren mahangar masana da kuma yadda Mata ke kallon illar ta hayaƙin girki ga lafiyarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....