Kasuwanci

Faɗuwar darajar Naira na shafar kasuwancin dabbobi a iyakar Najeriya da Nijar

Informações:

Synopsis

'Shirin Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba yadda harkokin kasuwanci ke tafiya a kasuwar dabbobi ta ƙasa da ƙasa da ke Maigatari ta Jihar Jigawa, wato kan iyakar Najeriya da Nijar, da kuma jin irin ƙalubalen da kasuwar ke fuskanta. Kasuwar ta Maigatari wadda ke iyakar Najeriya da Nijar na daya daga cikin manyan kasuwannin dabbobi a yankin arewacin Najeriya, domin ana sayar da nau'ikan dabbobi da suka hadar da shanu, raƙuma, dawaki, tumaki, awaki da jakkai sama da miliyan biyu a ranakun Alhamis din ko wanne mako, kuma yan kasuwa daga sassan Najeriya, Nijar da kuma Mali na zuwa a duk mako.