Dandalin Fasahar Fina-finai
Rayuwar Alhaji Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi
- Author: Vários
- Narrator: Vários
- Publisher: Podcast
- Duration: 0:20:00
- More information
Informações:
Synopsis
Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna’ ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya.Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama. Hawa Kabir a cikin shirin dandalin fasahar fina-fanai ta jiyo ta bakin wasu daga cikin mutanen Danjuma Katsina wanda ke daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama.Kasagi ya bada gudumawa sosai wajen daga darajar wasan kwaikwayo da ake sawa a wancan lokaci a Gidan Rediyo da talabijin Kaduna, yayin da littafin sa na ‘Kulba Na Barna’ ya shiga cikin jerin litattafan adabin da suka dauke hankalin dalibai da masu sha’awar karance karance na wancan lokaci.