Synopsis
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
Episodes
-
Bayani kan kotun ICC da kuma sammacin kamo firaministan Isra'ila da shugabannin Hamas
25/05/2024 Duration: 20minShirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a game da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC da batun sammacin kama firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da wasu shugabannin ƙungiyar Hamas. Ku latsa alamar sautin donjin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.........
-
Bayani a kan kamanceceniyar mulkin gurguzu da kama-karya
04/05/2024 Duration: 20minShirin, wanda ke zuwa muku duk mako a lokacin irin wannan, yana kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wasu daga cikin masu bibiyanmu suka aiko mana ne, kuma a yau, za ku ji amsar tambayar da ke neman ƙarin bayani a kan salon mulkin gurguzu, da kuma ko da gaske yana da kamanceceniya da mulkin kama-karya kamar yadda masu kushe shi ke fadi. Sai a kasance tare da mu.
-
Hukumar samar da wutar lantarki ta yi bayani game da kudin wuta da jama'a za su biya a Najeriya
13/04/2024 Duration: 20min‘Tambaya Da Amsa’ shiri ne da ke kawo amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Bayan janye tallafin lantarki a Najeriya, hukumar samar da wutar ta yi bayani game da rukunnai dabam dabam na masu amfani da wuta da abin da za su biya a matsayin kudin wuta. A yi mun ƙarin bayani a kan wadannan rukunnai. Menene ya sa dole sai an kasa al’umma zuwa rukuni -rukuni?